News
Gwamnatin Lagos Ta Rufe Wata Coci Saboda Damun Mutane Da Hayaniya

Hukumar kula da muhalli ta Jihar Legas ta rufe cocin All Christians Gathering Ministry da ke Surulere, bisa zargin haddasa hayaniya da hana mazauna yankin barci da daddare.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, bayan binciken da jami’an hukumar suka gudanar ya tabbatar da karya dokokin muhalli.
IAR ta samar da gajerun irin dawa domin taimaka wa manoma a yankunan da ke fama da matsalar tsaro
Ya ce za a ci gaba da rufe cocin da ke lamba 1, Ishola Street, har sai an ba da wani sabon umarni.
Matakin ya biyo bayan korafe-korafen wani mazaunin yankin da ya koka kan yadda hayaniyar ibadar cocin ke hana shi da sauran maƙwabta samun barci, musamman da tsakar dare.
Wahab ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba, yana mai cewa babu wani mutum ko cibiya da ta fi ƙarfin doka.
Ya kuma buƙaci dukkan cibiyoyin addini da kasuwanci su kiyaye dokokin muhalli, musamman waɗanda suka shafi hayaniya.
Dokokin muhalli na jihar sun kayyade hayaniyar da aka amince da ita a yankunan zama da decibel 55 da rana, da kuma decibel 45 da dare.
-
News7 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News4 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News7 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
