Connect with us

News

Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutane 37, Sama Da 3,000 Sun Kamu A Borno

Published

on

66016124 66016123

Akalla mutane 37 ne su ka mutu ya yin da sama da 3,000 su ka kamu da cutar kwalara a fadin kananan hukumomi bakwai na jihar Borno a watan Mayun nan, kamar yadda hukumomi su ka bayyana.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da gudunmuwar lafiya ta jihar Borno Dakta Saleh Kaza ne ya tabbatar da alkaluman a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban hadari ga lafiyar al’umma da ke bukatar daukar matakan gaggawa.

Advertisement

Peter Obi Ya Zaɓi Kwankwaso A Matsayin Abokin Takararsa

Kaza ya ce an samu rahoton bullar cutar a ranar 1 ga watan Mayu, kuma a ka tabbatar da ita a ranar 4 ga watan na Mayu, yana mai cewa alkaluman sun shafi tun daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa ranar 29 ga watan na Mayu, inda sama da mutane 3,000 su ka kamu da cutar da ya yin da mutane 37 su ka mutu a unguwanni 36 a kananan hukumomi bakwai da abin ya shafa.

Advertisement

Dr Kaza ya bayyana cewa a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan an samu sabbin mutane sama da 100 da su ka kamu, inda karamar hukumar Maiduguri ta fi kowacce kamuwa da cutar, inda mutane fiye da 2,000 su ka kamu, ya yin da Jere ke biye mata baya da mutane sama da 1,000.

Sauran kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Mafa, Konduga, Monguno, Ngala, da Magumeri, inda cutar ta shafi kauyuka sama da 138. yana mai cewa daukar matakin gaggawa na da matukar muhimmanci don yakar yaduwar cutar.

Advertisement

Hukumomin lafiyar sun danganta saurin yaduwar cutar da rashin tsaftar muhalli, da kuma lokacin damina da aka shiga, inda ambaliyar ruwa ke iya kwashe kazanta tare da kai ta cikin muhallan mutane.

Ya shawarci mazauna yankin da su kula da wanke hannayensu da ruwa da sabulu akai-akai, gujewa bahaya a fili, zubar da shara barkatai, da kuma tsaftace abinci kafin a ci, inda ya bukaci gaggauta kai rahoton wanda a ka gani da alamun amai da gudawa ga cibiyoyin lafiya mafi kusa.

Advertisement

Dr Kaza ya bayyana cewa gwamnati tana kokarin ganin an samar da allurar rigakafin cutar kwalara a jihar nan ba da dadewa ba,Sai dai ya jaddada cewa allura ba za ta taba maye gurbin tsaftar muhalli da ta jiki ba..

 

Advertisement

 

Vanguard

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending