Connect with us

News

Farashin Fetur Na Iya Sauka Zuwa Naira 900 Kan Kowace Lita  —Masana

Published

on

petr

Masana a harkar man fetur sun bayyana cewa farashin litar fetur (PMS) a Najeriya na iya sauka zuwa kusan naira 900 idan har shirin sulhu tsakanin Amurka da Iran ya tabbata tare da ci gaba da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Wannan na zuwa ne yayin da farashin danyen mai ya sauka daga sama da dala 120 kan ganga a watan Afrilu zuwa kusan dala 87 a halin yanzu, lamarin da masana suka danganta da raguwar zaman dar-dar da ya dabaibaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Advertisement

Farashin Fetur Na Iya Sauka Zuwa Naira 900 Kan Kowace Lita  —Masana

Masu harkar man fetur sun ce ci gaba da saukar farashin danyen mai da kuma yiwuwar sake bude mashigin ruwa na Hormuz na iya haifar da raguwar farashin fetur, dizal da kuma man jiragen sama a kasuwanni.

Advertisement

An samu tashin farashin danyen mai ne bayan rikicin Amurka da Iran ya barke a watan Fabrairu, inda farashinsa ya haura dala 100 kan ganga, har ma ya kai sama da dala 120 a wasu lokuta. Hakan ya haddasa tashin farashin makamashi a sassa daban-daban na duniya.

A Najeriya kuwa, farashin fetur ya tashi daga kusan naira 830 zuwa sama da naira 1,300 kan kowace lita, yayin da dizal da man jiragen sama su ma suka yi tashin gwauron zabo.

Advertisement

Wata majiya daga Matatar Dangote, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce akwai yiwuwar farashin fetur ya sauka zuwa naira 900 idan farashin danyen mai ya ci gaba da raguwa.

Majiyar ta ce duk da haka, har yanzu matatar na da tarin danyen man da aka saya a lokacin da farashinsa ya yi tsada, wanda hakan na iya jinkirta rage farashin cikin gaggawa.

Advertisement

“Farashin fetur na iya kaiwa naira 900 kan kowace lita idan farashin mai ya ci gaba da sauka a kasuwannin duniya. Sai dai har yanzu muna da danyen man da aka saya da tsada,” in ji majiyar.

Masana sun yi hasashen cewa idan yarjejeniyar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta yi nasara, aka sake bude mashigin Hormuz tare da daidaituwar kasuwar danyen mai, farashin fetur a Najeriya na iya ci gaba da faduwa a watanni masu zuwa.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending