Connect with us

News

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

Published

on

9d72ca 9978c1ed2eb5422f868d15d604cb57e1mv2 750x536

Gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da wasu takunkuman da ta kakaba wa Iran kan harkokin man fetur na tsawon kwanaki 60, a wani mataki da ake kallon zai taimaka wajen bunƙasa tattaunawar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin sanarwar da Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta fitar a ranar Litinin, an amince wa Iran ta ci gaba da samarwa, sayarwa da jigilar ɗanyen mai da sauran kayayyakin man fetur har zuwa ranar 21 ga Agustan 2026. Haka kuma, an ba da damar gudanar da wasu mu’amaloli da suka shafi harkokin sufuri, inshora da kuɗaɗen ciniki da a baya suke ƙarƙashin takunkumi.

Advertisement

Manchester United Ta Mallaki Filin Gina Sabon Filin Wasa Mai Daukar Mutane Dubu Dari 

Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan ci gaban da aka samu a tattaunawar zaman lafiya da ke gudana tsakanin Washington da Tehran. Ya ƙara da cewa Iran ta nuna aniyar ba da haɗin kai wajen tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz tare da amincewa da binciken Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Advertisement

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin rage zaman ɗar-ɗar da ya daɗe tsakanin ƙasashen biyu kan batutuwan nukiliya, tsaro da makamashi, waɗanda suka kasance manyan abubuwan saɓani a tsawon shekaru.

Masana harkokin makamashi na ganin cewa sassauta takunkumin na ɗan lokaci zai ƙara yawan man da Iran ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya, lamarin da ya riga ya fara tasiri wajen saukar da farashin mai a kasuwannin duniya.

Advertisement

Sai dai har yanzu ana sa ran makomar wannan sassauci za ta dogara ne da sakamakon tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu da kuma irin yadda Iran za ta cika alƙawuran da ta ɗauka

 

Advertisement

 

LEADERSHIP 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending