Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Riƙa Biyan Ma’aikata Tallafin Sufuri Naira 70,000 Duk Wata

Published

on

Shugaba Tinubu ya bayyana makomar TETFUND da NITDA da NASENI
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da biyan tallafin sufuri na Naira 70,000 duk wata ga ma’aikatan gwamnati a dukkan matakai, na tsawon watanni shida, daga watan Nuwamba 2026.

An cimma wannan matsaya ne a wani taron sasanci tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026.

Rashin Shakar Iska Ne Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Masu Hakar Ma’adinai 37 A Hannun Jami’an NSCDC —Kwamitin bincike

Baya ga tallafin sufuri, gwamnatin ta kuma amince da biyan wasu basussukan alawus-alawus na musamman da ma’aikata suka cancanci samu tun daga ranar 1 ga Mayu, 2026.

A cewar yarjejeniyar, za a fara biyan waɗannan kuɗaɗe kashi-kashi daga watan Nuwamba.

Sai dai, ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan ranar fara aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.

Advertisement

Duk da haka, sun amince da kafa wani kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin, wanda zai fara aiki nan take domin ci gaba da tattaunawa kan batun.

Tattaunawar ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafen ƙungiyoyin ƙwadago game da tsadar rayuwa, walwalar ma’aikata da kuma rashin cika wasu yarjejeniyoyin da aka cimma a baya.

Takardar yarjejeniyar da ɓangarorin suka rattaba wa hannu ta kuma ƙunshi batutuwan albashin ma’aikatan lafiya, rangwamen haraji da kuma alawus-alawus na haɗari ga jami’an aikin gona.

Sai dai, takardar ba ta fayyace takamaiman ranar da za a riƙa biyan tallafin sufuri a kowane wata ba, haka kuma ba ta bayyana cikakkun hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da biyan kuɗaɗen ba.

 

PUNCH

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending