Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Amince Ya Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Da Yuro Biliyan 1.04

Published

on

Tinubu 1000x600
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don ciyo bashin Dala biliyan 20.5

Shugaba Nijeriya Bola Tinubu ya aika da bukatar ga Majalisar Dattawa domin ta amince da sabon shirin karɓar bashin ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 20.5 da kuma Yuro biliyan 1.04.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito matakin na buƙatar amincewar sanatoci kafin a iya aiwatar da shirin kamar yadda doka ta tanada..

An Kwantar Da Dalibai 64 A Asibiti Bayan Shan Maganin Cutar Bilharzia A Katsina

A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa, musamman a fannonin wutar lantarki, sufuri, lafiya, ilimi, noma, samar da ruwan sha, tsaro da samar da ayyukan yi.

Tinubu ya kuma ce za a ware wani ɓangare na kuɗaɗen domin aiwatar da sauye-sauye a harkokin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

Advertisement

Bayan karanta wasiƙar, Akpabio ya miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Haruna Manu, domin gudanar da cikakken bincike kafin ɗaukar mataki.

Kwamitocin majalisar da ke kula da kasafin kuɗi da harkokin kuɗi za su kuma bayar da gudummawa wajen nazarin buƙatar.

Ana sa ran nazarin kwamitin zai taimaka wajen tantance yadda sabon shirin bashin zai dace da tsarin kula da basussukan Nijeriya da kuma lokacin da za a fara sakin kuɗaɗen domin aiwatar da ayyukan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending