Uncategorized
Uwar Gidan Gwamnan Kebbi Ta Jagoranci Gangamin Wayar Da Kai Kan Cutar Daji, Ta Ba Matan ’Yan Kasuwa Tallafin Naira Miliyan 20
Daga Khadijat Saidu, Birnin Kebbi
Uwar gidan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nafisa Nasir Idris, ta jagoranci tafiyar wayar da kan jama’a kan cutar daji ta shekarar 2026 a Birnin Kebbi, inda ta bayar da tallafin Naira miliyan 20 ga matan ’yan kasuwa domin ƙarfafa sana’o’insu.
Dakta Nafisa, wadda ita ce shugabar gidauniyar NANAS, ta jagoranci tafiyar ne a ranar Talata, daga Gidan Gwamnati zuwa filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.
Tafiyar ta samu halartar uwar gidan Mataimakin Gwamna, uwar gidan Sakataren Gwamnatin Jiha, matan kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi, da kuma matan masu ba wa gwamna shawara.
Sauran mahalarta sun haɗa da ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin fararen hula, ɗalibai, manyan jami’an gwamnati da abokan hulɗar ɓangaren lafiya.
Da take jawabi a wajen taron, Dakta Nafisa ta jaddada muhimmancin motsa jiki akai-akai da kuma zuwa asibiti domin duba lafiya, tana mai bayyana cewa gano cutar daji da wuri na taimakawa wajen samun ingantaccen magani.
Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a game da cutar, musamman kan hanyoyin gano ta da wuri da kuma neman kulawar likitoci.
Uwar gidan gwamnan ta kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa masu fama da cutar ta hanyar gidauniyarta ta NANAS.
A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiya na jihar, Kwamared Yakubu Samaila Augie, ya yaba wa Dakta Nafisa bisa ci gaba da gudanar da shirin wayar da kan jama’a kan cutar daji har tsawon shekaru uku.
Wani muhimmin ɓangare na taron shi ne baje kolin EMPOWER HER, inda Dakta Nafisa ta duba kayayyakin da matan suka gabatar, tare da bayar da tallafin Naira miliyan 20 domin taimaka wa matan ’yan kasuwa wajen bunƙasa sana’o’insu.
Haka kuma, an gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan lafiya, gwajin cutar kyauta da kuma nishaɗi, inda taurarin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka bayar da gudummawa.

