News
Kotu Ta Umarci A Ƙwace Kadarorin Naira Biliyan 212.8 Da Aka Alaƙanta Da Tsohon AGF, Abubakar Malami
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace sama da kadarori 40 da ake alaƙanta su da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.
Hukuncin ya fito ne a ranar Laraba, inda Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da buƙatar da Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar.
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ware Naira Biliyan 3.6 Domin Tallafa Wa Masu Sana’ar Ɗinki
Kotun ta bayyana cewa Malami da sauran waɗanda suka yi iƙirarin mallakar kadarorin sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji da za su tabbatar cewa an mallaki kadarorin ne ta hanyoyin da doka ta amince da su.
Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami da wasu daga cikin iyalansa tare da wasu kamfanoni suka gabatar, tana mai cewa buƙatun ba su da ingantaccen tushe a shari’a.
Mai Shari’a Abdulmalik ta ce abin da kotun ta fi mayar da hankali a kai ba wai tantance wanda ya mallaki kadarorin ba ne, sai dai binciken ko kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin sun fito ne daga halastattun hanyoyi.
Ta ƙara da cewa waɗanda ake ƙara sun kasa rushe zargin da EFCC ta gabatar cewa an mallaki kadarorin ne da kuɗaɗen da ake zargin sun samo asali ne ta haramtacciyar hanya.
Sai dai kotun ta jaddada cewa umarnin ƙwace kadarorin ba yana nufin an samu Abubakar Malami ko wani daga cikin waɗanda ake tuhuma da laifin aikata laifi ba ne.
A halin yanzu, tsohon Ministan Shari’ar, tare da matarsa da ɗansa, na ci gaba da fuskantar shari’a kan zargin halasta kuɗaɗen da ake zargin sun kai Naira biliyan 8.7.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
