Connect with us

News

Hisbah Ta Haramta Sana’ar Tura Fina-finai Da Waƙoƙi A Kano

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana’ar tura fina-finai da waƙoƙi (downloading) a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Sanarwar ta fito ne ta hannun Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahidden Aminuddeen, inda ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan ta gano cewa wasu masu wannan sana’a na amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.

“Boka Ne Ya Umarce Ni Na Kashe Ƙanwar Mahaifina Da ’Ya’yanta Shida” — Umar Auwalu A Kotu

Ya ce hukumar ba za ta amince da ci gaba da irin waɗannan ayyuka ba, saboda haka ta haramta gudanar da sana’ar a faɗin jihar.

Haka kuma, ya bayyana cewa an umarci jami’an Hisbah su kama duk wanda aka samu yana gudanar da sana’ar, domin a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

Hukumar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba ta haɗin kai wajen tabbatar da bin wannan umarni da kuma kare tarbiyya a cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending