News
Gwamnatin Tarrayya Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Harajin Man Fetur
Ministan kuɗin Najeriya Taiwo Oyedele ya ce da zaran tattalin arzikin ƙasar ya inganta, gwamnati za ta gabatar da sabon harajin man fetur domin samun kuɗaɗen da za ta gina hanyoyi da kuma inganta waɗanda ake da su.
Oyedele ya ce irin wannan haraji ya na aiki a wasu ƙasashe daga kashi 20 zuwa 80, yayin da ƙasashen Afirka ke sanya tsakanin ƙashi shida zuwa 10.
Ministan ya ce kuskure ne a sanya harajin gab da lokacin da gwamnati ta cire tallafin mai, domin hakan zai sanya ta ta biya harajin a madadin ƴan ƙasa saboda kaucewa jefa su cikin ƙuncin rayuwa.
Oyedele ya ce sun ɗauki matakin ƙin aiwatar da harajin ne domin inganta rayuwar jama’ar ƙasar musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Ministan ya ce da zaran abubuwa sun inganta kuma tattalin arzikin ƙasa ya tsaya da kafufuwan sa, za su aiwatar da harajin, duk da ya ke ba haka su ke so ba.
Oyedele ya ce harajin da za’a tara a wannan ɓangaren za’a karkata shi ne zuwa aikin gyara hanyoyi da kuma ci gaban ƙasa, baya ga amfani da kudin wajen daidaita farashin albarkatun man.
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News2 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
