News
Kotu Ta Yi Watsi Da Karar El-rufai Ta Neman Diyyar Naira Miliyan 120 Kan DSS, EFCC Da ICPC
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar neman diyya ta naira miliyan 120 da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, ya shigar kan DSS da wasu hukumomi uku bisa zargin sa ido da sauraron wayarsa ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Sylvanus Oriji ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa ƙarar ba ta da hujjar da za ta sa kotu ta amince da ita.
Kotu ce Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar ‘Yan Takarar Da Cire Daga Jerin Sunaye — INEC
Kotun ta kuma umarci El-Rufai ya biya kowace daga cikin hukumomin huɗun naira 200,000 a matsayin kuɗin shari’a, waɗanda suka haɗa da DSS, Hukumar EFCC, Hukumar ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
A hukuncinsa, alƙalin ya ce wasiƙun gayyatar da EFCC da ICPC suka aika wa tsohon gwamnan domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi masa ba su keta haƙƙoƙinsa na asali ba.
Game da yunƙurin kama El-Rufai da DSS ta yi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kotun ta amince da hujjar hukumar cewa tana da ikon sanya sunayen waɗanda take son bincika a jerin waɗanda ake sa ido a kansu, tare da kama su idan akwai buƙata.
Kotun ta kuma yi watsi da hujjar El-Rufai cewa yunƙurin kama shi ya saɓa wa doka saboda babu sammacin kama shi. Haka kuma, ta ce kwace fasfo ɗinsa na ƙasashen waje da DSS ta yi ya kasance cikin ikon da doka ta ba hukumar.
A ƙarshe, kotun ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya, tare da bayyana cewa El-Rufai bai gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da zarge-zargensa ba.
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News2 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
