News
Kotu Ce Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar ‘Yan Takarar Da Hukumar Ta Cire Daga Jerin Sunaye — INEC
Hukumar zaɓe INEC ta bayyana cewa kotuna ne za su yanke hukunci na ƙarshe kan cancantar ’yan takarar da ba’a saka sunayensu cikin jerin ’yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi na zaɓen 2027 ba.
Hukumar ta bai wa jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da abin ya shafa wa’adin kwanaki 14 domin shigar da ƙorafi, idan suna ganin an cire sunayensu ba bisa ƙa’ida ba, wa’adin da zai kare a ranar 24 ga Oktoba, 2026.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya ce hukumar ba ita ta soke cancantar ’yan takarar kai tsaye ba, sai dai jam’iyyun da suka kasa cika wasu sharuɗɗan doka sun rasa damar gabatar da ’yan takara.
Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da wajabcin miƙa rajistar mambobin jam’iyya, ciki har da sunayen ’yan takarar da suka shiga zaɓen fidda gwani, ga hukumar zaɓe cikin wa’adin da aka tsara.
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News2 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
