Connect with us

News

Dawo Da Tallafin Fetur Zai Iya Mayar da Farashin Fetur Naira 4,000 Kan Lita — Musa Illiyasu Kwankwaso

Published

on

Musa Iliyasu Kwankwaso

Wani jigo a Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC, Dr Musa Illiyasu Kwankwaso, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin man fetur da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ke goyon baya, na iya ƙara wa Najeriya matsin tattalin arziki.

Kwankwaso, wanda shi ne Daraktan Kuɗi na Hukumar Kula da Kogin Hadejia-Jama’are, ya ce dawo da tsarin tallafin fetur na baya zai iya ƙara nauyin kashe kuɗin gwamnati, tare da rage kuɗaɗen da ake warewa ayyukan raya ƙasa.

IITA Ta Horar Da Manoma Sama Da 1,800 Kan Sabbin Dabarun Noman Zamani A  Kano ‎

A cewarsa, cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar da inganta ajiyar kuɗaɗen waje, yayin da jihohi suka samu damar biyan albashin ma’aikata da gudanar da ayyukan more rayuwa.

Ya bayyana cewa dawo da tallafin na iya shafar kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen ilimi, kiwon lafiya, fansho, albashi da gina ababen more rayuwa.

Kwankwaso ya kuma yi gargaɗin cewa sauya manufar cire tallafin na iya sake haifar da dogayen layukan neman fetur a gidajen mai, tare da ƙara wa gwamnati wahalar cika wasu wajibai na kuɗi.

Advertisement

Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa, ciki har da hanyar bakin teku ta Legas zuwa Kalaba, da manyan hanyoyin Kano zuwa Abuja da Kano zuwa Maiduguri.

Sai dai ya jaddada cewa ya kamata a auna batun dawo da tallafin bisa yadda za a samar da kuɗaɗen aiwatar da shi, ba tare da sake jefa ƙasar cikin matsin kuɗi ba.

Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya su ƙi amincewa da manufofin Atiku, tare da ci gaba da goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending