News
Cin Hanci Ya Mayar da Kotunan Najeriya Kasuwannin Sayar da Hukunci — Tsohuwar Alƙaliyar Kotun Ƙoli
Tsohuwar alƙaliyar Kotun Ƙoli ta Najeriya, Mai Shari’a Amina Adamu Augie, ta yi gargaɗin cewa cin hanci da rashawa a ɓangaren shari’a na mayar da kotunan ƙasar tamkar kasuwannin sayar da hukunci, maimakon wuraren da ake neman adalci.
Amina Augie ta bayyana hakan ne a Abuja, yayin wani taron tunawa da cika shekaru 40 da kammala karatu na ɗaliban Makarantar Koyon Aikin Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law School) na shekarar 1986.
NDLEA Ta Kama Matar Da Ta Ɓoye Tabar Wiwi A Cikin Galan Mai A Kano
Ta ce rashawa da ake zargin tana faruwa tsakanin wasu alƙalai, lauyoyi da ma’aikatan kotu na lalata martabar ɓangaren shari’a tare da rage amincewar jama’a ga tsarin shari’ar ƙasar.
A cewarta, ko da mutane kaɗan ne ke aikata irin waɗannan laifuka, hakan na iya jefa mutuncin dukkan ɓangaren shari’a cikin haɗari, ciki har da waɗanda ke gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana.
Tsohuwar alƙaliyar ta kuma bayyana katsalandan ɗin siyasa, ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyuka da kuma jinkirin shari’o’i a matsayin manyan ƙalubalen da ke hana jama’a samun adalci cikin sauƙi.
Ta jaddada cewa rashin cikakken ’yancin cin gashin kai na ɓangaren shari’a na iya kawo cikas ga gudanar da adalci, musamman idan kotuna sun dogara da gwamnatin zartarwa wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Amina Augie ta yi kira da a ɗauki matakin ladabtarwa da hukunta duk wani alƙali ko lauya da aka tabbatar da aikata laifi, ba tare da la’akari da matsayinsa ko girman mukaminsa ba.
Ta ce hakan na da muhimmanci wajen dawo da amincewar jama’a ga kotuna da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da shari’a bisa gaskiya da adalci.
Haka kuma, ta buƙaci a ƙarfafa ’yancin cin gashin kan ɓangaren shari’a, a ɗauki matakan rage jinkirin shari’o’i, tare da tabbatar da cewa kowa yana ƙarƙashin doka, ba tare da wani mutum ya fi ƙarfin hukuncinta ba.
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News1 day ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
