News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ware Naira Biliyan 3.6 Domin Tallafa Wa Masu Sana’ar Ɗinki
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ware Naira biliyan 3.6 domin tallafa wa masu sana’ar ɗinki a faɗin ƙasar nan, a wani yunƙuri na bunƙasa sana’o’in hannu, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya.
An ware kuɗin ne a ƙarƙashin shirin Skill Up Artisans (SUPA) da Asusun Horar da Ma’aikata na Ƙasa (Industrial Training Fund – ITF) ke aiwatarwa domin inganta ƙwarewar matasa da masu sana’o’in hannu.
Hisbah Ta Haramta Sana’ar Tura Fina-finai Da Waƙoƙi A Kano
Babban Daraktan ITF, Dakta Afiz Ogun, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da tantance masu neman shiga shirin SUPA na shekarar 2026.
Ya ce manufar tantancewar ita ce tabbatar da cewa ƙwararrun masu sana’a ne kawai za su amfana da shirin, domin tabbatar da ingancin horon da kuma cimma burin gwamnati na bunƙasa sana’o’in hannu.
A cewarsa, waɗanda suka yi nasarar shiga shirin za su samu horo na zamani tare da takardun shaidar ƙwarewa na ƙasa da na duniya. Haka kuma, za a haɗa wasu da masu ɗaukar aiki, yayin da za a taimaka wa wasu wajen kafa ko faɗaɗa sana’o’insu ta hanyar shirin bunƙasa kasuwanci.
Dakta Ogun ya bayyana cewa masu sana’ar ɗinki ne suka fi yawa cikin dubban waɗanda suka nemi shiga shirin, lamarin da ya sa aka ware Naira biliyan 3.6 domin tallafa musu wajen inganta sana’arsu da ƙara yawan abin da suke samarwa.
Ya ce shirin SUPA na daga cikin matakan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na rage rashin aikin yi, haɓaka ƙwarewar matasa da ƙarfafa ci gaban tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bunƙasa sana’o’in hannu.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
