News
JAMB Ta Soke Karatun Digirin Hadin Gwiwa Da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta sanar da dakatar da shigar dalibai zuwa shirye-shiryen digiri da Kwalejojin Ilimi (Colleges of Education) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar jami’o’i.
Sabon matakin, wanda zai fara aiki daga zangon karatu na 2026/2027, ya mayar da Takardar Koyarwa ta Najeriya (NCE) a matsayin babbar hanyar shiga da karatu a kwalejojin ilimin.
Iran Ta Ce Dole Ne A Kawo Ƙarshen Rikicin Da Ke Tsakanin Isra’ila Da Lebanon Kafin Cimma Yarjejeniya
JAMB ta bayyana cewa matakin na da nufin ƙarfafa darajar NCE da kuma mayar da hankali kan ainihin manufar kwalejojin ilimi wato horar da malamai masu ƙwarewa.
Wannan na nufin cewa daga sabuwar shekarar karatu, daliban da ke son shiga kwalejojin ilimi za su fi mayar da hankali ne ga shirye-shiryen NCE maimakon shirye-shiryen digiri da ake gudanarwa ta hanyar alaƙa da jami’o’i.
Masana na ganin matakin zai iya taimakawa wajen farfaɗo da sha’awar karatun NCE, yayin da wasu ke nuna damuwa kan yadda hakan zai shafi ɗaliban da ke neman samun digiri kai tsaye ta kwalejojin ilimi.
