Connect with us

News

Iran Ta Ce Dole Ne A Kawo Ƙarshen Rikicin Da Ke Tsakanin Isra’ila Da Lebanon Kafin Cimma Yarjejeniya

Published

on

2026 06 21T184355Z 2011284866 RC2CYLAZV7BF RTRMADP 3 IRAN CRISIS

Iran ta gargaɗi Amurka da ta yi hankali bayan Shugabanta, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soja kan Tehran saboda goyon bayan da take bai wa Hezbollah a Lebanon.

Trump, ya ce Amurka za ta iya kai hari kan Iran idan har ba ta daina tallafa wa abin da ya kira “wakilanta” a Lebanon da ke haddasa matsala ba.

Advertisement

“Ba Shekaru A Ofis Ke Nuna Ƙwarewa Ba’ — Muhawara Ta Kunno Kai Kan Waiya Da Garba”

A martaninsa, babban mai shiga tsakani daga Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce sojojin Iran a shirye suke, kuma ya gargaɗi Amurka da ta guji kalamai masu tsauri, yana mai cewa za su mayar da martani idan aka kai mata hari.

Advertisement

Wannan musayar kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke tattaunawa a Switzerland kan yadda za a kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Tattaunawar na da nufin samar da tsarin yarjejeniyar zaman lafiya, amma har yanzu akwai ƙalubale.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending