Connect with us

News

Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida

Published

on

Sirika

Wata babbar shaida da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana yadda aka yi amfani da jirgin kamfanin Ethiopian Airlines, aka yi masa ado da tambarin “Nigeria Air”, domin nuna kamar an kaddamar da kamfanin jirgin saman ƙasa.

Shaidar, Christopher Odofin, wanda shi ne mai gabatar da ƙara na 12, ya shaida a gaban Mai Shari’a S. C. Oriji cewa an shigo da jirgin zuwa Abuja a ranar 27 ga Mayu, 2023, inda aka yi amfani da shi na ɗan lokaci kaɗan don nuna wa jama’a, sannan aka mayar da shi Addis Ababa a ranar 29 ga Mayu, 2023, ranar mika mulki.

Advertisement

Adadin Falasdinawan Da Suka Rasu A Hare Haren Isra’ila A Gaza Ya Kai 72,991

A cewarsa, binciken EFCC ya gano cewa an kulla yarjejeniya da kamfanin Ethiopian Airlines ne kwanaki biyar kacal kafin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bar ofis. Ya ce an kuma shirya amfani da ma’aikatan kamfanin na Habasha tare da wasu mutane da aka sanya musu kayan “Nigeria Air” domin yin hotuna da gabatar da aikin a matsayin kamfanin ƙasa.

Advertisement

Shaidar ta kuma bayyana cewa an samu karin kuɗin kwangilar kafa kamfanin “Nigeria Air” daga sama da Naira miliyan 299 zuwa fiye da Naira miliyan 599, bisa umarnin da ake zargin tsohon ministan ya bayar.

EFCC na zargin cewa an yi amfani da wannan tsarin ne domin yaudarar jama’a da kuma bai wa aikin kamannin kamfanin jirgin sama na ƙasa, duk da cewa jirgin mallakin Ethiopian Airlines ne aka yi amfani da shi.

Advertisement

Hukumar ta kuma ce tana ci gaba da gurfanar da Hadi Sirika da wasu da ake tuhuma a gaban kotu, inda shari’ar ke ci gaba.

Alkalin kotun, Mai Shari’a S. C. Oriji, ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga Yuni, 2026.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending