News
Kotu Ta Yanke Wa Wasu Mutum Uku Da Aka Samu Da Laifin Yin Garkuwa Da Mutane Hukuncin Kisa
Babban kotun jihar Adamawa ta yanke wa wasu maza uku hukuncin kisa bayan an kama su da laifin yin garkuwa da fastoci biyu a Fabrairu 2025 a jihar.
Alkalin kotun Christopher Mapeo ya sanar inda sanarwar ya nuna cewa kotun ta kama Taledo Demiel, Namomai Medan da Mikaila Yusuf da laifin yin garkuwa da wasu fastocin cocin darikan Katolika biyu da suka hada da Matthew Dutsemi da Abraham Sauman.
An gurfanar da wadannan mutane bisa laifukkan hada baki domin yin garkuwa, yin garkuwa da mutane, fashi da makami da neman a biya kudin diyyar mutanen da suke tsare da su.
An yi garkuwa da wadannan farstoci ranar 22 ga Fabrairu 2025 a gidajen su dake Gwaida-Malam a karamar hukumar Numan.
A lokacin rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da yin garkuwa da fastocin inda ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarnin gudanar da bincike domin ceto mutane tare da kamo masu garkuwa da mutanen.
Hukumar SSS ta jihar ta bayyana cewa, wannan hukunci yakara yawan adadin hukunce-hukuncen kisa da hukumar ta samu a shekarar 2026 zuwa bakwai.
Bisa rahotanin da hukumar tsaron ta fitar rahotannin da suka yi tsokaci kan sanarwar ta SSS, wannan hukunci na baya-bayan nan ya biyo bayan wasu hukunce-hukuncen kisa da dama da aka samu a jihohi daban-daban a bana, da suka hada da shari’o’in da suka shafi garkuwa da mutane, ta’addanci, da sauran manyan laifuka.
Raranar 20 ga Mayu babban kotu dake jihar Ekiti ta yanke wa Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar hukuncin kisa bisa laifin yin garkuwa da mutane.
A ranar 3 Yuni babban kotun Gwamnatin Tarayya dake Babban Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa wasu maza hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama su da laifin kashe mutane da dama a harin da suka kai wa cocin St. Francis na Katolika dake Owo a jihar Ondo hari a watan Yuni 2022.
Wani babban kotu dake jihar Katsina ta yanke wa wata mata Hauwa’u Mukthar hukuncin kisa ranar 15 ga Yuni sannan a jihar Kogi babban kotu ta yanke wa Jibrin Haloli hukuncin kisa ranar 16 ga Yuni bisa laifin yin garkuwa da kashe makwabcin sa.
A jihar Sokoto a ranar 22 ga Yuni babban kotu ta yanke wa Muhammed Yusuf Sallau, Jabbi Ahlaji Yale da Kabiru Muhammed hukuncin kisa bisa laifukkan da suka shafi ta’adda ci da jigilar makamai.
A ranar 28 ga Satumba zuwa babban kotu dake jihar Sokoto ta yanke wa Ibrahim Usman wanda aka fi saninsa da sunan Dan Iyali hukuncin kisa bisa alakarsa da kashe da yin garkuwa da wasu mutane uku.
Wannan hukuncin kisa na jihar Adamawa ya kara yawan hukunce-hukuncen kisan da ake samu a Najeriya musamman yanzu da jami’an tsaro ke yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran muggan ayyuka.
-
News14 hours ago
Wani Jami’an Dansanda Ya Kashe Abokiyar Aikinsa Kuma Ya Kashe Kansa A Kogi
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News7 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

