News
EFCC ta kama ‘yan China 14 A Masanaʼantun Sarrafa Lithium Ba Bisa Ka’ida Ba
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta Nijeriya (EFCC) ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya guda ɗaya a masana’antun sarrafa lithium guda huɗu da ke yankin Ogere a Jihar Ogun.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a yau Litinin.
A cewar EFCC, jami’an hukumar na ofishin shiyyarta na Lagos Zonal Directorate 2 ne suka gudanar da samamen a ranar Jumma’a, 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da gudanar da sa ido.
Hukumar ta ce jami’anta sun kwato buhunan duwatsun lithium, wayoyin hannu guda 18, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda huɗu, na’urorin karɓar tashoshin talabijin guda biyu, na’urar sarrafa talabijin da kuma motar dakon kaya kirar tirela daga wuraren.
-
News15 hours ago
Wani Jami’an Dansanda Ya Kashe Abokiyar Aikinsa Kuma Ya Kashe Kansa A Kogi
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News11 hours ago
Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Kare Kansa Kan Zargin Sauraron Wayar Nuhu Ribadu

