News
JIBWIS Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Agajin Da Ya Nemi A Ba Su AK47 Su Kai Hari
JIBWIS Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Agajin Da Ya Nemi A Ba Su AK47 Su Kai Hari
Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ga wani mutum sanye da kayan aikin agajin gaggawa na ƙungiyar yana neman a ba su bindigogin AK-47 domin kai hari a Enugu.
Sheikh Bala Lau ya buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa su gano waɗanda ke da hannu a lamarin, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.
Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Kare Kansa Kan Zargin Sauraron Wayar Nuhu Ribadu
A cikin wata sanarwa kan lamarin, shugaban JIBWIS ya bayyana cewa ƙungiyar ba ta da alaƙa da kalaman da aka ji a bidiyon, yana mai cewa irin waɗannan kalamai da ke ƙunshe da barazanar tashin hankali sun saɓa wa koyarwa da manufofin ƙungiyar.
Ya ce kasancewar mutum sanye da kayan aikin agajin gaggawa na JIBWIS ba ya nufin yana magana ne a madadin ƙungiyar ko kuma yana da izininta.
Sheikh Bala Lau ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar wasu mutane na ƙoƙarin ɓata sunan ƙungiyar ta hanyar irin wannan lamari, sai dai ya jaddada buƙatar gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Ya bayyana cewa JIBWIS ta daɗe tana ƙoƙarin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, yana mai nuni da wani taron ƙasa da ƙasa da ƙungiyar ta shirya a Abuja, wanda ya haɗa shugabannin Kiristoci da malaman Musulunci daga mazhabobi daban-daban.
A cewarsa, ƙungiyar ta shafe kusan shekaru 48 tana gudanar da ayyukan wa’azi, ilimi da jin ƙai, tare da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin al’umma ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko yankin da mutane suka fito ba.
Ya buƙaci hukumomin tsaro su binciki asalin bidiyon, mutanen da suka bayyana a cikinsa da kuma ko suna da wata alaƙa da ƙungiyar, domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
-
News11 hours ago
Wani Jami’an Dansanda Ya Kashe Abokiyar Aikinsa Kuma Ya Kashe Kansa A Kogi
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

