News
Mutane 842 Sun Mutu, An Yi Garkuwa Da 279 A Watan Mayu – Rahoto
Wani rahoto da cibiyar bincike ta Nextier Nigeria ta fitar ya bayyana cewa aƙalla mutum 842 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka yi garkuwa da 279 a faɗin Najeriya cikin watan Mayun shekarar 2026 sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi sassan ƙasar.
Rahoton ya nuna cewa an samu jimillar tashe-tashen hankula 156 a watan da aka yi nazari a kai, lamarin da ya nuna ci gaba da tabarbarewar yanayin tsaro a wasu yankunan Najeriya.
Yadda HE Garo Ya Wakilci Gwamna Fiye Da Wadansu Mataimakan Da Gwamnoninsu Cikin Kwanaki 47
A cewar rahoton, yawan hare-haren da suka shafi rashin tsaro ya ƙaru da kusan kashi 51.1 cikin ɗari idan aka kwatanta da watannin baya, yayin da yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ya karu da kashi 19.7 cikin ɗari.
Masu binciken, waɗanda suka haɗa da masana harkokin tsaro da manufofin gwamnati tare da wasu malamai daga Nnamdi Azikiwe University, sun bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da suka wallafa kan halin tsaro a ƙasar.
Rahoton mai taken “Matsalar Tsaron Najeriya: Matsayinta Da Kuma Yadda Ta Yi Ƙamari” ya yi nazari kan yadda matsalolin tsaro suka sauya tun daga farkon shekarar 2026 zuwa watan Mayu, tare da bayyana manyan barazanar tsaro da ke fuskantar ƙasar.
Bugu da ƙari, rahoton ya gabatar da wasu shawarwari ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro kan hanyoyin da za a bi wajen dakile ayyukan masu tayar da ƙayar baya, garkuwa da mutane da sauran laifuffukan da suka shafi rashin tsaro.
Masu binciken sun jaddada cewa akwai buƙatar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, al’umma da masu tsara manufofi domin rage yawaitar hare-hare da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
