News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ƙarin Albashin Kashi 80 Ga Dakarun Soji
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙarin albashi ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce na inganta jin daɗin jami’an tsaro da ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata ta bayyana cewa kimanin jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumban 2026.
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
A cewar sanarwar, jami’an da ke daga mukamin Brigadier Janar zuwa Janar za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin ɗari, yayin da jami’an daga mukamin Kanal zuwa Warrant Officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin ɗari. Haka kuma, sojojin da ke daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su amfana da ƙarin albashi mafi girma na kashi 80 cikin ɗari.
Sanarwar ta ƙara da cewa sabon tsarin zai ƙara yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa kan albashin jami’an sojin daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924 a duk shekara.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar sojin wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan ƙasar.
Ya ce, “Mazan da matan da ke tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinmu sun cancanci a tallafa musu tare da nuna musu godiya saboda hidimar da suke yi wa ƙasa. Gwamnatinmu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin jami’an tsaro tare da samar musu da makamai da fasahohin zamani domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.”
Shugaban ya kuma jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa ba tare da ingantaccen tsaro ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da dukkan rundunonin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Tinubu ya kuma yi kira ga jami’an rundunar sojin da su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alamar godiya daga gwamnati bisa irin hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa Najeriya za ta yi nasara kan masu neman tada zaune tsaye da tarwatsa zaman lafiyar ƙasar.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
