News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai shekaru 35, Habibu Bello, bisa zargin kasancewa mamba a ƙungiyar masu garkuwa da mutane da kuma fashi da makami da satar shanu da ke aiki a tsakanin jihohin Kano, Kaduna da Katsina.
An kama Bello ne a ranar 14 ga Satumba, 2026, bayan rundunar ta samu sahihan bayanan sirri.
An Kama Mai PoS da Ake Zargi Da Taimakon Mai Garkuwa Da Mutane A Katsina
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce binciken da aka gudanar bayan kama wanda ake zargin ya kai ga cafke wani mutum mai suna Mudam, mazaunin Kwanar Dangora, wanda ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyar.
A cewar rundunar, Bello ya amsa cewa yana da hannu a wasu hare-haren garkuwa da mutane, ciki har da sace Hajiya Binta daga Kwanar Dangora, inda aka biya Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa.
Rundunar ta kuma ce wanda ake zargin yana da hannu a ayyukan satar shanu da wasu laifuka a Kano, Kaduna da Katsina.
Kakakin rundunar ya ce ana ci gaba da bincike domin gano asalin drone ɗin da kuma mai shi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame, musamman a yankunan da ke kan iyakar Kano da jihohin makwabta.
