News
Daga Cikin Masu Neman Aikin Kwastam 573,680, Mutum 3,852 Kacal A Ka Dauka
Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta bayyana sunayen mutum 3,852 da suka yi nasara a aikin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2024/2025, bayan karɓar buƙatun aiki daga mutum 573,680 a faɗin ƙasar.
Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Ya ce yawan waɗanda suka samu aikin ya kai kashi 0.67 cikin 100 na duk masu neman aikin.
KACCIMA Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Masu Ƙananan Sana’o’i Da Matashiya TV Ta Shirya A Kano
A cewarsa, daga yanzu hukumar za ta riƙa gudanar da ɗaukar sabbin ma’aikata a kowace shekara domin cike guraben da ke samuwa sakamakon ritayar ma’aikata, tare da inganta tsarin gudanar da aikin ba tare da tsaiko ba.
Adeniyi ya bayyana cewa an bi ƙa’idojin da suka shafi rabon guraben aiki tsakanin jihohi da kuma cancanta, yana mai ƙara da cewa duk waɗanda suka yi nasara za su ci gaba da gwaje-gwajen lafiya da tantancewa kafin a ba su aikin a hukumance.
Ya kuma gargaɗi masu neman aiki da su guji biyan kuɗi ga duk wanda ya yi musu alƙawarin samun aiki, yana jaddada cewa ɗaukar ma’aikatan Kwastam kyauta ne kuma ana yin sa ne bisa cancanta, tare da sanar da cewa za a buɗe sabon shirin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2026 nan gaba a wannan shekarar.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
-
News1 day ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
