News
Bayan Watanni Shida, An Ceto Mutane 176 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kwara
Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da ceto mutane 176 da aka yi garkuwa da su tun bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai garuruwan Woro da Nuku da ke Karamar Hukumar Kaiama a ranar 3 ga Fabrairu, lamarin da ya kawo karshen kusan watanni shida da suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Laraba, gwamnatin ta bayyana nasarar a matsayin babban ci gaba wajen yaki da rashin tsaro, inda ta yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da jami’an tsaro da kuma duk wadanda suka bayar da gudunmawa wajen nasarar aikin ceto.
Daga Cikin Masu Neman Aikin Kwastam 573,680, Mutum 3,852 Kacal A Ka Dauka
Ko da yake ba a bayyana cikakken yadda aka gudanar da aikin ba, majiyoyi daga yankin sun shaida cewa jami’an tsaro, tare da rakiyar motocin soji da tankokin yaki, sun gudanar da wani samame a cikin dazuka kafin daga bisani aka kubutar da wadanda aka sace. Rahotanni sun ce an mika mutanen da aka ceto ga hukumomin gwamnati domin kula da su.
Wani mazaunin yankin, Aliyu Umar, ya ce al’ummomin yankin sun ga ayarin motocin jami’an tsaro suna shiga cikin daji, kuma bayanan da suka samu sun tabbatar da cewa an yi nasarar ceto mutanen. Ya ce har zuwa lokacin da yake magana ba su gana da wadanda aka ceto ba, amma dukkan bayanan da suke samu sun tabbatar da cewa suna hannun jami’an gwamnati.
An yi garkuwa da mutanen ne a lokacin mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai garuruwan Woro da Nuku a ranar 3 ga Fabrairu, inda aka kashe mutane da dama, aka raba iyalai da muhallansu tare da lalata gidaje da ababen more rayuwa. Wannan nasara ta zo ne kwanaki biyar bayan rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun ki karbar fiye da Naira miliyan 155 da iyalan wadanda abin ya shafa suka tara domin neman a sako su.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
