Connect with us

News

Majalisar Ɗinkin Duniya ta musanta zargin yiwa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya

Published

on

000 A4EG8KE

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rashin adalci daga shugabanni a Najeriya a dai-dai lokacin da ƴan ta’adda ke ci gaba da kai hare-hare musamman guraren Ibada ne, babban dalilin da ya sanya duniya ke kallon matsalolin da ke faruwa a Najeriya a matsayin kisan ƙare dangi.

A cikin wani rahoto da Majalisar ta fitar, ta ce rashin ɗaukar mataki mai ƙarfi kan masu aikata laifi da kuma kisan al’umma daga mahukunta na sake jefa gwamnatin Najeriya cikin shakkun sakaci da rayukan jama’a.

Advertisement

Gwamantin legas Ta Kwace Babura Okada Sama Da  270

Ƙunshin rahoton Majalisar ya kuma ci gaba da cewa idan aka kalli matsalolin da ke faruwa a ƙasar, babu laifin fararen hula idan sun kwatanta shi da yunƙurin kisan ƙare dangi da gwamnati ke goyon baya ta hanyar zuba idanu.

Advertisement

Babbar jami’ar sashen tattara bayanan ƙasashe kan ƴancin addinai ta Majalisar Nazila Ghanea ce ta bayyana haka, bayan binciken da ya biyo bayan zargin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana yiwa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

 

Advertisement

Nazila wadda ta ziyarci Najeriya mai mafi yawan Musulmi a arewaci da mafi yanwan Kiristoci a kudanci, ta ce ƴan tawagarta sun tattauna da mutane sama da 200 a Abuja, Kano, da kuma Plateau, kuma abinda suka gano shine kowanne ɓangare yana jin jiki ba wai iya mabiya addinin Kirista ba.

Yayin tattaunawar ta da Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, Nazila ta ce ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke bayyana cewa suna yaƙi da Kiristoci dukkansu a arewacin ƙasar suke, don haka sun fi kisan Musulmi fiye da Kiristoci a wannan yanki.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending