News
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
Hukumomin da ke kula da shari’ar yara a Jihar Kano sun bayyana cewa yara 24 da ake zargi da aikata laifuka sun amfana da shirin gyaran tarbiyya maimakon gurfanar da su a kotu a cikin watan Yuli.
Shugaban Dandalin Haɗin Gwiwa na Kula da Shari’ar Yara a Kano, wanda kuma shi ne Babban Lauyan Gwamnati kuma Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Salisu Tahir, ne ya bayyana hakan bayan taron dandalin na wata-wata da aka gudanar a ranar Alhamis.
Muna Da Ikon Dakatar Da Asusun Gwamnatin Jiha Har Na Tsawon Sa’o’i 72 Kafin Umarnin Kotu — EFCC
Daraktan Gurfanar da Masu Laifi na Ma’aikatar Shari’a, Abdullahi Ibrahim Muhammad, wanda ya wakilce shi, ya ce an samu wannan nasara ne ta hanyar shirin karkatar da yara daga bin tsarin shari’ar kotu zuwa hanyoyin gyaran hali.
Ya ce daga cikin yara 24 da suka ci gajiyar shirin, Ma’aikatar Shari’a ta Kano ta kula da shari’o’i 18, yayin da Hukumar Hisbah ta jihar ta kula da sauran guda shida.
A cewarsa, shari’o’in 18 da Ma’aikatar Shari’a ta karɓa sun fito ne daga kotunan majistare huɗu da ke sauraron shari’ar yara. Ya kuma bayyana cewa daga cikin yara shida da Hisbah ta kula da su, uku an mayar da su ga iyalansu, biyu kuma an miƙa su ga rundunar ’yan sanda, yayin da aka saki ɗaya ba tare da wani sharadi ba.
Abdullahi Muhammad ya ce shirin karkatar da yara daga shari’ar kotu yana ba su damar samun gyaran hali ta hanyar ilimantarwa, ba da shawara , maimakon fuskantar hukuncin kotu da zai iya shafar makomarsu.
Ya ƙara da cewa manufar shirin ita ce gyara tarbiyyar yara da ba su wata dama ta sake komawa rayuwa mai kyau, maimakon hukunta su kawai.
Ya ce shirin na samun goyon bayan Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano tare da tallafin Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), domin ƙarfafa tsarin shari’ar da ya dace da yara bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
