News
An Kama Mutum Takwas Saboda Yada Labaran Karya A Najeriya
Hukumomin tsaro a Najeriya sun kama aƙalla mutum takwas bisa zargin yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ke haifar da ruɗani a kafafen sada zumunta, yayin da gwamnati ke ƙara ɗaukar tsauraran matakai kan masu amfani da intanet wajen yaɗa bayanan da ba su da tushe.
Kamen ya biyo bayan yaɗuwar wasu saƙonni da bidiyoyi marasa sahihanci da suka shafi sace ɗalibai a Jihar Oyo, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba tare da tayar da hankalin iyalai da al’ummar yankin.
Ana Zargin Wata Amarya Ta Hallaka Mijinta Da Wuƙa Watanni Biyu Bayan Aurensu A Kano
Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara sun kai hari makarantu uku a jihar, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da ma’aikata da dama. Bayan faruwar lamarin, kafafen sada zumunta sun cika da jita-jita da bayanan da ba a tantance ba, ciki har da iƙirarin cewa an kashe wasu daga cikin waɗanda aka sace.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo, Olushola Alayande, ya ce jami’ansa sun gano fiye da wallafe-wallafe 15 masu ɗauke da bayanan da ke ruɗar da jama’a.
A cewarsa, mafi yawan saƙonnin sun ƙunshi zarge-zarge marasa tushe, sake yaɗa tsofaffin bidiyoyi da ba su da alaƙa da lamarin, da kuma gabatar da jita-jita a matsayin tabbatattun labarai.
Yadda Labaran Ƙarya Ke Haifar Da Illa
Hukumomi sun bayyana cewa yaɗa bayanan ƙarya na iya haddasa tashin hankali da asarar rayuka. Misali, a Jihar Legas, wasu fusatattun matasa sun kashe wani matashi mai sana’ar babur bayan yaɗuwar wani saƙon ƙarya da ke iƙirarin cewa wasu ‘yan bindiga na mamaye wasu sassan birnin.
Rahotanni sun ce an kama mutum 15 dangane da wannan lamari.
Tinubu Da Manyan Jami’ai Na Fuskantar Jita-jita
Baya ga al’amuran tsaro, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na daga cikin manyan jami’an gwamnati da ke yawan fuskantar yaɗuwar labaran ƙarya musamman yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara karatowa.
A baya-bayan nan ma rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata wani bidiyo da aka kirkira ta hanyar fasahar AI, wanda aka yaɗa a shafukan sada zumunta tare da iƙirarin cewa Hafsan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, ya amince da gazawar dabarun magance matsalolin tsaro.
Masana harkokin sadarwa sun yi gargadin cewa ƙaruwar amfani da fasahar kirkirar bidiyo da murya ta AI na ƙara sauƙaƙa wa masu yaɗa bayanan ƙarya aikin ruɗar da jama’a.
Dokar Intanet Na Tanadin Hukunci
Yawancin waɗanda aka kama ana tuhumarsu ne ƙarƙashin Dokar Laifukan Intanet ta Najeriya (Cybercrimes Act), wadda ta haramta yaɗa bayanan ƙarya a kafafen sadarwa.
Dokar ta tanadi hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari ko kuma tarar har naira miliyan bakwai ga duk wanda aka samu da laifin yaɗa bayanan ƙarya da ka iya haddasa ruɗani ko barazana ga tsaron jama’a.
Hukumomin tsaro sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika tantance sahihancin bayanai daga kafafen da suka dace kafin su yada su, domin kauce wa haddasa matsaloli da tayar da hankalin al’umma.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
