Connect with us

News

INEC Ta Wallafa Bayanai: Tinubu Bai Cika Guraben Firamare Da Sakandare A Fom Din Takararsa Ba

Published

on

Tinubu Bola 750x430

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa bayanan sirri da takardun shaidar ‘yan takarar shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta ƙasa domin zaɓen shekarar 2027, kamar yadda Sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanada.

Bayanan da aka liƙa a hedikwatar ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan sun ƙunshi sunayen ‘yan takara, jinsinsu, adireshin zama, cancantar karatu, tarihin ayyukansu da kuma bayanan ‘yan takarar mataimakan shugaban ƙasa.

Binciken bayanan ya nuna cewa ɗan takarar jam’iyyar APC kuma Shugaban Ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, bai cike guraben da aka tanada domin bayanan makarantar firamare da ta sakandare ba. Maimakon haka, ya bayyana ne kawai cewa ya samu digirin farko (BSc) daga Chicago State University (CSU) a shekarar 1979, tare da haɗa kwafin takardar shaidarsa.

Batun takardar shaidar Tinubu daga CSU ya taɓa haifar da muhawara gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da aka yi ta ce-ce-ku-ce kan wasu bayanan da suka shafi tarihin karatunsa.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cikakken tarihin karatunsa tun daga makarantar firamare da sakandare har zuwa jami’a. Haka kuma, ɗan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya samu First School Leaving Certificate a 1954 da West African School Certificate a 1961, sannan ya kammala digirin MA a fannin International Relations a shekarar 2020.

INEC ta ce wallafa bayanan na bai wa jama’a damar tantance takardun da ‘yan takara suka gabatar tare da ba masu ƙorafi damar bin hanyoyin doka idan suna da wata shakka kan bayanan da aka bayyana.

Advertisement

 

 

THE CABLE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending