News
INEC Ta Cire Sunayen Mutane Miliyan Daya Da Dubu Dari Shida Daga Kundin Masu Zabe

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta cire rajistar masu zaɓe 1,608,660 da aka gano ba su inganta ba, bayan kammala nazarin rajistar zaɓe ta wucin gadi.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Kotu Ta Wanke Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa A Kano Bayan Shekaru Biyar
Amupitan ya ce hukumar ta karɓi bayanan rajistar masu zaɓe 11,088,238 a matakai uku na aikin rajistar shekarar 2025/2026.
Ya ƙara da cewa na’urar tantance bayanan halittu (Automated Biometric Identification System) ta gano rajista 1,545,052 da ke buƙatar ƙarin bincike, sai dai ya jaddada cewa hakan ba yana nufin an soke rajistarsu kai tsaye ba.
Haka kuma, hukumar ta cire bayanan mutane 876 da aka tabbatar sun rasu, tare da gano wasu 873, lamarin da ya kai adadin bayanan mamatan da aka cire zuwa 1,749.
Wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafen da aka gabatar kan rajistar zaɓen da hukumar ta baje wa jama’a daga ranar 9 zuwa 15 ga Oktoba, 2026.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa jami’an rajista 54 a jihohi 10 na iya fuskantar matakin ladabtarwa ko gurfanarwa a gaban kotu bisa zargin hannu a kura-kuran da aka gano.
INEC ta ce za ta wallafa sabuwar rajistar masu zaɓe a ranar 16 ga Disamba, 2026.
