Connect with us

News

KANO: ’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Rogo

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun sace shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Rogo ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Fanka Beli, a wani hari da suka kai garin Beli da ke ƙaramar hukumar.

Rahotanni daga majiyoyi a yankin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 11:00 zuwa 11:30 na daren Litinin, inda ’yan bindigar da ake zargin sun shiga garin, kafin su yi awon gaba da shugaban jam’iyyar.

Mutum 1,000 Sun Kamu Da Cutar Mashako A  Katsina

Majiyoyin sun kuma ce ’yan bindigar sun kashe mutane biyu a yayin harin, lamarin da ya jefa mazauna garin cikin fargaba da tashin hankali.

Wata majiya daga yankin ta ce har zuwa yanzu ba a samu cikakken bayani kan inda aka tafi da Alhaji Abdullahi Fanka ko halin da yake ciki ba.

“Har yanzu ba mu san inda aka kai shi ba. Muna fatan jami’an tsaro za su iya gano inda yake tare da kubutar da shi,” in ji majiyar.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da faruwar harin ba.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin gano inda shugaban jam’iyyar yake da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar garin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending