News
GECCI Ta Bukaci Gwamnati Ta Inganta Manufofin Kiwo Domin Tallafa Wa Makiyaya
Daga Safiya Muhammad Usman
Hukumar Gandun Daji tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Global Environment and Climate Conservation Initiative (GECCI) sun gudanar da taron bita na kwana ɗaya kan hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen samar da ingantattun manufofi da za su bunƙasa harkokin kiwo da inganta rayuwar makiyaya a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar GECCI, Abdul Hamid Tahir Hamid, ya ce an shirya bitar ne domin duba yadda za a yi amfani da ilimin gargajiya tare da haɗa shi da sabbin dabarun kiwo domin inganta rayuwar makiyaya, kare muhalli da kuma tabbatar da tsaron al’ummomin da ke dogaro da harkar kiwo.
Ya ce taron ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki damar tattauna hanyoyin da za a shawo kan matsalolin da ke hana ci gaban fannin kiwo a ƙasar.
Mahalarta taron daga wasu jihohin Arewacin Najeriya sun bayyana cewa makiyaya na ci gaba da fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ƙarancin filayen kiwo, rashin wadataccen ruwa ga dabbobi, ƙarancin cibiyoyin kula da lafiyar dabbobi da kuma illolin sauyin yanayi.
Sun buƙaci gwamnati ta ƙara zuba jari a fannin kiwo ta hanyar samar da hanyoyin kiwo na zamani, gina wuraren samar da ruwa ga dabbobi, ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar dabbobi da kuma horas da makiyaya kan sabbin dabarun kiwo masu kare muhalli.
Shugaban ƙungiyar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu wajen aiwatar da manufofin da za su inganta zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma, tare da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Wakiliyarmu, Safiya Muhammad Usman, ta ruwaito cewa mahalarta taron sun bayyana fatan cewa shawarwarin da suka fito da su za su taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen da ke addabar fannin kiwo a Najeriya.
