Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kama Mutum Biyu Bisa  Zargi Da Sayar Da Filayen Gwamnati A Rimin Zakara

Published

on

IMG 20260730 WA0249 768x432

Gwamnatin Jihar Kano ta kama mutane biyu da ake zargi da yanka tare da sayar da filayen gwamnati da ke Rimin Zakara a Ƙaramar Hukumar Ungogo.

Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Birane ta Jihar Kano, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai.

An Cafke Wani Matashi Bisa Zargin Yunƙurin Satar Adaidaita Sahu A Kano

Ya ce waɗanda aka kama na daga cikin mutanen da ake zargi da hannu wajen mamaye da sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.

A cewarsa, bayan matakan da gwamnati ta ɗauka domin kawo ƙarshen rikicin filayen Rimin Zakara, waɗanda ake zargin sun koma yankin Gundutse South Terminal da ke Ƙaramar Hukumar Kura domin ci gaba da wannan haramtacciyar harka.

Ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Muhammad Kabir, mai shekara 57 daga Gaida, da Kamilu Iliyasu, mai shekara 55 daga Zoo Road, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da neman Mustapha Matazu, wanda ake zargi ya tsere.

Advertisement

Kwamishinan ya yi Allah-wadai da ci gaba da mamaye da sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamo da gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan laifuka.

Haka kuma ya buƙaci al’umma su riƙa tantance sahihancin kowanne fili ta hanyar tuntubar Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Birane kafin su saya, domin kauce wa faɗawa hannun masu damfara.

 

 

INDEPENDENT POST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending