Connect with us

News

NLC Ta Yaba Wa Ma’aikatan Da Suka Mayar Da Albashin Da Aka Biya Sau Biyu A Kano

Published

on

20260731 180911 COLLAGE

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta roƙi ma’aikatan gwamnati da su kwantar da hankalinsu tare da yin haƙuri kan jinkirin da aka samu wajen biyan albashin wasu ma’aikata, sakamakon wata matsalar fasaha da ta afku a bankin da ke kula da biyan albashin.

Shugaban NLC na Kano, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matsalar ta faru ne yayin Bayanan albashin ma’aikata.

Gwamnatin Kano Ta Kama Mutum Biyu Bisa  Zargi Da Sayar Da Filayen Gwamnati A Rimin Zakara

Ya ce kuskuren ya sa wasu ma’aikata sun karɓi albashinsu sau biyu, yayin da bankin ya cire ƙarin kuɗin da aka tura musu bisa kuskure. Haka kuma, wasu ma’aikatan har yanzu ba su karɓi albashinsu ba saboda matsalar.

Ya ce ƙungiyar na fahimtar damuwar da hakan ya haifar wa ma’aikata, amma ta na roƙonsu da su ƙara haƙuri, domin hukumomin gwamnati na aiki tuƙuru wajen magance matsalar.

A cewarsa, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Akanta Janar da Sakataren Gwamnatin Jihar suna haɗa kai da bankin domin tabbatar da cewa duk ma’aikatan da abin ya shafa sun karɓi albashinsu cikin gaggawa.

Advertisement

Kwamared Inuwa ya kuma yabawa ma’aikatan da suka mayar da kuɗaɗen da aka tura musu sau biyu bisa kuskure, yana mai cewa hakan ya nuna gaskiya, riƙon amana da biyayya ga doka.

Ya ce irin wannan haɗin kai zai taimaka wajen gaggauta warware matsalar tare da daidaita tsarin biyan albashin ma’aikata.

Shugaban NLC ɗin ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da biyan albashin ma’aikata a kan lokaci duk da ƙalubalen da aka fuskanta.

A ƙarshe, ya yi kira ga ma’aikata da su guji yaɗa jita-jita ko ɗaukar matakan da za su iya tayar da hankalin jama’a, yana mai jaddada cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar cikin gaggawa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending