Uncategorized
An Daura Auren Kamaldeen Adamu Da Khadija Samisu A Garin Kura
An daura auren Kamaldeen Adamu, ɗan Alhaji Adamu Yusuf Ganga, da amaryarsa Khadija Samisu Muhammad, ‘yar Alhaji Saminu Muhammad Kura, a ranar Juma’a, 31 ga Yuli, 2026, a Masallacin Juma’a na Umar Bin Abdul’aziz JIBWIS, da ke Kofar Arewa a garin Kura, Jihar Kano.
Bikin daurin auren ya samu halartar malamai, ‘yan uwa, abokai da sauran masu fatan alheri daga sassa daban-daban, waɗanda suka taru domin shaida wannan muhimmin lamari tare da yi wa ma’auratan addu’ar samun zaman lafiya da albarka.
Gwamnatin Kano Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargi Da Sayar Da Filayen Gwamnati A Rimin Zakara
An gudanar da daurin auren cikin natsuwa da bin koyarwar addinin Musulunci, inda aka roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya sanya albarka a rayuwar sabbin ma’auratan, Ya ba su zaman lafiya, soyayya, fahimtar juna da zuri’a ta gari.
Mahalarta bikin sun taya iyalan Alhaji Adamu Yusuf Ganga da na Alhaji Saminu Muhammad Kura murnar wannan farin ciki, tare da yi musu fatan alheri da ɗorewar zumunci tsakanin iyalan biyu.
Allah Ya sanya wannan aure ya zama mai albarka, Ya kuma sa ya kasance mafarin rayuwa mai cike da farin ciki, rahama da ci gaba ga ma’auratan. Ameen.
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
