News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Ango Dauke Da Ƙullin Hodar Ibilis 72 A Filin Jirgin Sama
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta kama wani sabon ango ɗan shekara 25 da ake zargi da ƙoƙarin safarar ƙulli 72 na hodar ibilis zuwa Portugal.
An kama matashin a babban ɗakin tantance matafiya na filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, yayin da yake ƙoƙarin shiga jirgin Ethiopian Airlines zuwa Portugal ta Addis Ababa.
KANO: Mutane 18 Sun Jikkata Yayin Da Mahaukacin Kare Ya Cije Su A Garko – NFSS
A cewar NDLEA, wanda ake zargin ya haɗiye ƙullin hodar ibilis ɗin kafin kama shi. Daga bisani an sanya shi ƙarƙashin kulawa, inda ya fitar da ƙullin 72 ta duburarsa.
Hukumar ta ce wanda ake zargin ya shaida wa jami’anta cewa a baya yana sana’ar ƙawata motoci a Trade Fair Complex da ke Ojo, Jihar Legas, kafin ya koma Portugal a watan Mayun 2023.
NDLEA ta ce matashin ya dawo Najeriya a kwanan nan, inda ya yi aure a ranar 13 ga Satumba, 2026. Hukumar ta ce ana zargin ya shiga safarar miyagun ƙwayoyi ne domin neman kuɗin biyan basussukan da suka taru a kansa yayin shirye-shiryen bikin aurensa.
Hukumar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da wanda ake zargin ke hannun jami’anta domin ɗaukar matakin da ya dace.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
