Connect with us

News

KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga

Published

on

IMG 20260831 WA0001

’Yan mata uku ’yan gida ɗaya sun mutu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a Dam ɗin Tiga da ke Jihar Kano.

Matan, waɗanda suka fito daga garin Yalwan Rugu-Rugu da ke Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, sun rasu ne a ranar Asabar, 29 ga Agustan 2026.

Gwamnan Plateau Ya Hana Ayyukan HISBA A Jos

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, kamar yadda bayanai daga ’yan uwan mamatan suka bayyana.

Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Kano (ALGON), Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijama’a, ce ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.

Matan da suka mutu sun haɗa da Murjanatu, Atikatu da Bilkisu, wadda aka fi sani da Amira. Dukkansu ’yan gida ɗaya ne.

Advertisement

Hajiya Sa’adatu ta jajanta wa iyalan mamatan da al’ummar yankin, tare da addu’ar Allah Ya jiƙan su da rahama, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending