News
KANO : ’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Rogo
Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun sace shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Rogo ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Fanka Beli, a wani hari da suka kai garin Beli da ke ƙaramar hukumar.
Rahotanni daga majiyoyi a yankin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 11:00 zuwa 11:30 na daren Litinin, inda ’yan bindigar da ake zargin sun shiga garin, kafin su yi awon gaba da shugaban jam’iyyar.
Mutum 1,000 Sun Kamu Da Cutar Mashako A Katsina
Majiyoyin sun kuma ce ’yan bindigar sun kashe mutane biyu a yayin harin, lamarin da ya jefa mazauna garin cikin fargaba da tashin hankali.
Wata majiya daga yankin ta ce har zuwa yanzu ba a samu cikakken bayani kan inda aka tafi da Alhaji Abdullahi Fanka ko halin da yake ciki ba.
“Har yanzu ba mu san inda aka kai shi ba. Muna fatan jami’an tsaro za su iya gano inda yake tare da kubutar da shi,” in ji majiyar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da faruwar harin ba.
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
