News
Donald Duke Ya Sha Alwashin Magance Rashin Tsaro A Arewa Idan Ya Ci Zaben 2027
Fitaccen ɗan siyasar nan kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya idan ya yi nasara a zaɓen 2027.
Donald Duke ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya yi bayani kan matakan da zai ɗauka wajen magance rashin tsaro da kuma wasu matsalolin da suka shafi ci gaban Arewacin Najeriya.
Milo Ta Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 A Kano Da Jos
Ya bayyana talauci a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen taɓarɓarewar tsaro a Arewa, yana mai cewa matsalar ba za ta warware ta hanyar matakan tsaro kaɗai ba, sai an inganta tattalin arziki da samar wa jama’a hanyoyin dogaro da kai.
Duke ya ce gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar zamani wajen kula da iyakokin Najeriya, ciki har da amfani da jirage marasa matuƙa da tauraron ɗan Adam domin gano masu shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba da kuma bai wa jami’an tsaro damar ɗaukar mataki cikin sauri.
Ya ce duk da cewa akwai masu aikata laifuka da ke shigowa Najeriya daga wasu ƙasashe, yawancin matsalar ’yan bindiga ta samo asali ne daga cikin gida, don haka akwai buƙatar magance matsalolin cikin gida maimakon ɗora alhakin rashin tsaron gaba ɗaya kan baƙi.
A ɓangaren noma, Duke ya ce akwai madatsun ruwa tsakanin 300 zuwa 400, musamman a Arewacin Najeriya, waɗanda za a iya amfani da su wajen bunƙasa noman rani da samar da abinci a duk shekara idan aka farfaɗo da su tare da amfani da su yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana ma’adanai a matsayin wani muhimmin ɓangare na arzikin Arewa bayan noma, yana mai cewa akwai buƙatar tantance adadin ma’adanai da ake da su a jihohi domin samar da sahihan bayanan da za su jawo hankalin masu zuba jari.
Duke ya ce za a tsara harkar haƙar ma’adanai domin tabbatar da cewa al’ummomin da ake hako albarkatun a yankunansu, ƙananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya suna cin gajiyar su, tare da hana masu aikata laifuka amfani da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, Duke ya ce ilimi ya kamata ya zama wajibi kuma kyauta, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi da wata sana’a da za ta ba shi damar dogaro da kansa.
Ya kuma yi magana kan matsalar shan miyagun ƙwayoyi a Arewa, inda ya danganta yaɗuwarta da rashin aikin yi, takaici da rashin kyakkyawar makoma ga matasa, tare da cewa samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a na daga cikin hanyoyin rage matsalar.
Duke ya ce babban burinsa shi ne a mayar da kowace jiha cibiyar tattalin arziki, ba cibiyar gudanar da siyasa kawai ba, ta yadda jama’a za su samu damar aiki da bunƙasa rayuwarsu a jihohinsu ba tare da tilasta musu ƙaura zuwa Abuja, Lagos ko wasu manyan birane ba.
Ya kuma bayar da shawarar samar da wutar lantarki a matakin yankuna, inda ya ce samar da cibiyoyin makamashi a yankunan Sanatoci zai taimaka wajen kusantar da samar da wutar lantarki ga jama’a da bunƙasa tattalin arzikin yankunan ƙasar.
