News
Dalilin Da Suka Jawo Yara Sama Da 870,000 Ba Sa Zuwa Makaranta A Kano — Rahoto
Wani sabon bincike ya gano dalilan da suka sa kimanin yara 875,593 da ke tsakanin shekaru 5 zuwa 18 ba sa zuwa makaranta a jihar Kano duk da irin yadda iyaye a jihar ke goyon bayan ilimin zamani.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Ali Makoda, ne a ranar Alhamis ya gabatar da sakamakon binciken da aka kwashe watanni huɗu ana yi a yayin da yake ganawa da manema labarai.
Donald Duke Ya Sha Alwashin Magance Rashin Tsaro A Arewa Idan Ya Ci Zaben 2027
Kano na da kimanin yara miliyan 6.6 da suka kai shekarun zuwa makaranta, inda binciken ya nuna cewa kashi 13.4% daga cikin su ba sa zauwa makaranta.
Saɓanin zargin da aka daɗe ana yi cewa rashin son karatun boko ne ke haddasa matsalar ilimi a Arewa, binciken ya gano cewa kashi 99.6% na iyaye na ganin ilimi yana da muhimmanci ga ’ya’yansu.
Binciken, wanda aka gudanar a ƙananan hukumomi 44 na jihar, shi ne na farko da aka gudanar a Kano kan yaran da ba sa zuwa makaranta cikin sama da shekaru 10.
Ma’aikatar Ilimi ta Kano da Hukumar Kididdiga ta jihar ne suka gudanar da shi tare da haɗin gwuiwar shirin Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE), wanda gwamnatin Birtaniya ke tallafawa.
An yi binciken ne a kan gidaje 1,783 da ya shafi mutane 13,915 ciki har da yara 7,192 masu shekaru 5 zuwa 18. Daga cikinsu, yara 6,233, wato kashi 86.67% suna zuwa makaranta yayin da yara 959, wato kashi 13.34% ba sa makaranta.
Binciken ya gano cewa yara 501 ba su taɓa zuwa makaranta ba yayin da guda 458 suka daina zuwa makaranta bayan sun fara.
Matsalar kuɗi ce kan gaba:
Matsalar kuɗi ce ta fi hana yara zuwa makaranta, inda kashi 22.3% na iyaye suka ce ba sa iya biyan kuɗaɗen makarantar ‘ya’yansu. Rashin samun makaranta a kusa kuma ya shafi kashi 17.2%.
Nisan makaranta, ayyukan gida da ake sa yara, auren wuri da kai yara aikatau na daga cikin sauran abubuwan da ke hana yara samun ilimi.
Rahoton ya kuma nuna cewa riƙe yara a makaranta bayan sun shiga na gab da zama babban ƙalubale kamar shigar da su makaranta.
Maza sun fi yawa:
Binciken ya nuna cewa maza ne suka fi yawa cikin yaran da ba sa zuwa makaranta, inda suka kai kashi 54.2% yayin da mata suke da kashi 45.8%.
Masu binciken sun danganta hakan da matsin tattalin arziki da ke tilasta wa wasu yara maza neman aikin yi da kuma tasirin tsarin ilimin Tsangaya/Almajiri.
A tsarin karatun Almajiranci, wasu yara maza kan bar gidajensu ne domin koyon Alƙur’ani a wajen malamai. Sai dai wasu daga cikinsu kan ƙare a tituna suna bara ba tare da samun ingantaccen ilimin karatu, rubutu, lissafi da sana’a ba.
Bambanci tsakanin ƙananan hukumomi:
Matsalar ta bambanta sosai daga wata ƙaramar hukuma zuwa wata.
Ƙaramar hukumar Doguwa ce ta fi fama da matsalar da kashi 40%, Warawa da kashi 34.69%, Gaya kashi 33.86%, Sumaila kashi 28%, Wudil kashi 26.75%, Bichi kashi 25.83%, Ungogo kashi 21.65%, Kiru kashi 20.99%, Gezawa kashi 20.16% da Kumbotso mai kashi 19.85%.
A cewar masu binciken, wannan bambanci ya bai wa gwamnati damar mayar da hankali kan wuraren da matsalar ta fi tsanani musamman wajen samar da makarantu da tallafin gaggawa.
Rahoton ya ce matsalar ta samo asali ne daga abubuwa biyar:
-Matsin lambar iyali da al’adu (kashi 22.6%)
-Matsalar rashin kuɗi (kashi 20.8%)
-Matsalolin da suka shafi makarantun kansu (kashi 20%)
-Matsalolin da suka shafi yara kansu (kashei 18.3%)
-Rashin tsaro da sauran ƙalubale (kashi 18.2%).
Ba matsalar rashin son ilimi ba ce:
Kwamishinan Ilimi na Kano, Ali Makoda, ya ce bayanan binciken za su taimaka wajen gano wuraren da matsalar ta fi ƙamari da tsara matakan da za su ƙara yawan yaran da ke shiga makaranta.
Binciken ya kuma gano cewa kashi 90.9% na iyaye na goyon bayan bai wa yara maza da mata damar samun ilimi iri ɗaya.
Rahoton ya jaddada cewa matsalar ba rashin son karatu ba ne domin iyaye suna son ’ya’yansu su yi karatu, sai dai rashin isasshen tsarin da zai sa karatun ya yi sauƙi kuma mai inganci.
Masu ruwa da tsaki sun ce ana buƙatar haɗin gwuiwar gwamnati da masu tallafawa wajen magance talauci da samar da ababen more rayuwa da inganta tsaro domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da ƙoƙarin cimma muradan kawo cigaba mai ɗorewa (SDG 4) na 2030.
