Connect with us

News

2027: SERAP Ta Buƙaci INEC Ta Bayyana Adadin Kuɗaɗen Da Doka Ta Ƙayyade Wa Jam’iyyu Su Kashe Yayin Yaƙin Neman Zaɓe

Published

on

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam da tabbatar da gaskiya da adalci a Nijeriya, ta buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana adadin kuɗaɗen da doka ta ƙayyade wa jam’iyyun siyasa da ’yan takara domin gudanar da yaƙin neman zaɓe a babban zaɓen 2027.

SERAP ta buƙaci Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da ya yi amfani da ikon da dokar ƙasa ta ba hukumar wajen bayyana ainihin iyakar gudunmawar kuɗaɗen da aka halasta bayarwa a harkokin siyasa ƙarƙashin Sashe na 91 na Dokar Zaɓe ta 2026.

Donald Duke Ya Sha Alwashin Magance Rashin Tsaro A Arewa Idan Ya Ci Zaben 2027

Ƙungiyar ta kuma roƙi INEC ta wallafa wa jama’a cikakken bayani kan iyakokin kuɗaɗen da doka ta tanada, tare da sanar da jam’iyyun siyasa, ’yan takara, masu bayar da gudunmawa da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da bin dokar.

SERAP ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar neman bayanai mai taken “Freedom of Information Request”, wadda Mataimakin Daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya fitar ranar Asabar.

Ta kuma buƙaci INEC ta bayyana matakan da ta tanada domin sa ido, bincike da tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi gudunmawar kuɗaɗen siyasa da kuma iyakar kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe yayin da ƙasar ke shirin babban zaɓen 2027.

Advertisement

Ƙungiyar ta nemi hukumar ta bayyana yadda take sa ido kan harkokin kuɗaɗen zaɓe, ciki har da hanyoyin gano da kuma binciken gudunmawar da ake bayarwa ta tsabar kuɗi ko kuma ta hanyar asusun banki, domin tabbatar da sahihancin bayanan kuɗaɗen da jam’iyyu da ’yan takara ke amfani da su.

A cewar SERAP, tabbatar da gaskiya da adalci wajen samar da kuɗaɗen siyasa na da muhimmanci wajen gudanar da zaɓe cikin bin doka, tare da bai wa ’yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu ba tare da an rinjaye su da kuɗi ko wasu alfarma ba.

Buƙatar ta SERAP na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan INEC ta fara ayyukan da suka shafi tunkarar babban zaɓen 2027, yayin da ’yan takara da jam’iyyun siyasa a matakai daban-daban ke ƙara fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending