Connect with us

News

SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Hana Wike Rufe Ofisoshin Jakadanci 34 A Abuja

Published

on

Spread the love

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama da yaki da cin hanci ta SERAP ta bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, daga aiwatar da barazanar da ya yi na rufe ofisoshin jakadanci na ƙasashe 34 da ke Abuja.

SERAP ta yi wannan kira ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta jaddada cewa matakin da Wike ke shirin ɗauka yana da hadari ga martabar Najeriya a idon duniya, tare da barazana ga yarjejeniyoyin diflomasiyya da ƙasashen waje.

Ƴansanda sun kama mutum 27, sun ƙwato muggan makamai a Kaduna

Sanarwar ta bayyana cewa, “Rufe ofisoshin jakadanci ba wai kawai zai sabawa ƙa’idojin diflomasiyya ba ne, har ma yana iya janyo wa Najeriya koma-baya wajen huldar kasashen waje da kiyaye yarjejeniyoyin kasa da kasa da ta rattaba hannu a kansu.”

Hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) ce ta fara bankado lamarin, inda ta bayyana cewa ƙasashen da ke da ofisoshin jakadanci 34 suna bin bashin haya tun daga shekarar 2014, lamarin da ya sanya minista Wike yin barazanar rufe ofisoshin.

Advertisement

Wasu daga cikin ƙasashen da lamarin ya shafa sun haɗa da Ghana, Thailand, Equatorial Guinea, Côte d’Ivoire, Rasha, Philippines, Netherlands, Turkiyya, Guinea, Ireland, Uganda, Iraqi, Zambiya, Tanzaniya, Jamus, Kongo, Venezuela, Koriya, Trinidad da Tobago.

Sauran su ne Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Zimbabwe, Ethiopia, Indonesiya, Tarayyar Turai, Switzerland, Saudiyya, China da Afirka ta Kudu.

SERAP ta shawarci gwamnatin tarayya da ta bi hanyar diflomasiyya wajen warware wannan matsala, tare da tattaunawa da ofisoshin da abin ya shafa domin cimma mafita cikin ruwan sanyi.

Ta kara da cewa, “Yin gaggawar ɗaukar mataki cikin hayaniya da barazana na iya ƙara dagula al’amura, tare da jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya wajen hulɗar kasa da kasa.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *