News
Ƴansanda sun kama mutum 27, sun ƙwato muggan makamai a Kaduna
Ƴansanda a jihar Kaduna sun ce sun kama mutum 27 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daba-daban.
Wata sanarwar da mai magana da yawun ƴansandan jihar DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce an samu nasarar kama ɓata-garin ne bayan wani samame da ta kai maɓoyarsu a yankin Kawo.
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 13 Da Ake Zargi Da Ajalin Jami’in Sojan Ruwa Yayin Kwace Wayarsa
“Mun kai samamen ne jiya Lahadi a lungu da sako na yankin Kawo. Abin ya kai ga kama mutum 27 da ake zargi da aikata laifuka har ma da ƙwato muggan makamai,” in ji Mansir.
Ya ce cikin makaman da suka ƙwato sun haɗa da wuƙaƙe da adduna da fartanyu da kuma ƙunshin ganyayyaki da ake kyautata zaton tabar wiwi ce da kuma sauran kayan maye.
Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya ƙara nanata ƙoƙarin rundunar wajen ganin an mutunta doka da oda a faɗin jihar.
