Connect with us

News

Wani Matashi Dan Kano Ya Yanke Gaban Sa

Published

on

IMG 20260512 160633 866

Wani matashi ɗan asalin jihar Kano mai suna Sani, daga unguwar Tukuntawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, ya shiga wani mawuyacin hali a ƙasar Libya bayan da ya yanke gaban sa sakamakon matsalar ƙwaƙwalwa da ake zargin ya kamu da ita.

Rahotanni sun nuna cewa matashin ya tafi ƙasar Libya ne domin neman na kai, sai dai daga bisani ya fara fama da matsalar ƙwaƙwalwa yayin da yake aiki a wata ma’aikata a ƙasar.

Advertisement

Shugaba Tinubu Na Tattaunawa Da Bankin Duniya Kan Sabon Bashin Dala Biliyan 1.25 —Rahoto

Kakakin ƙungiyar Northern Nigerian Organization (NNO), ƙungiyar ’yan Arewacin Najeriya mazauna Libya, Abba Na-Gaida Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Advertisement

A cewarsa, matashin ya fara nuna alamun rashin lafiyar ƙwaƙwalwa tun watannin baya, lamarin da ya jefa abokan aikinsa da sauran ’yan Najeriya da ke tare da shi cikin damuwa.

Fagge ya bayyana cewa kafin aukuwar lamarin, matashin ya tuka wata motar katafila a kamfanin da yake aiki tare da rusa wani gini, abin da ya sa mahukuntan kamfanin suka bayar da umarnin killace shi domin hana afkuwar wata matsala.

Advertisement

“Bayan an killace shi ne sai aka ji yana ihu. Da aka duba shi kuma sai aka same shi cikin jini bayan ya yanke gaban sa,” in ji shi.

Ya kara da cewa lokacin da suka isa wajen, sun tarar da matashin cikin mawuyacin hali, inda ya yi asarar jini mai yawa.

Advertisement

“Da muka duba sai muka gano ya yanke gaban sa, saura kaɗan ya rage bai rabu gaba ɗaya da jikinsa ba. Lamarin ya tayar mana da hankali sosai,” a cewar Fagge.

Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin matsalar ƙwaƙwalwar da ta same shi ba, amma kungiyar tasu ta haɗa kuɗi domin kai shi asibiti cikin gaggawa domin ceton rayuwarsa.

Advertisement

A cewarsa, likitoci na shirin yi masa tiyata saboda sashen jikin bai gama yankewa gaba ɗaya ba.

Fagge ya kuma yi korafin cewa tun bayan fara lalacewar lafiyar matashin suka sanar da ofishin jakadancin Najeriya da ke Libya, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

Advertisement

Ya ce a yanzu haka matashin na kwance a asibiti yana samun kulawar likitoci, yayin da suke kokarin ganin an dawo da shi Najeriya domin ci gaba da yi masa magani.

“Idan ba a samu taimako daga gwamnati ba, za mu haɗa kuɗi tsakaninmu domin ɗaukar nauyin dawo da shi gida Kano ta jirgi,” in ji shi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending