Connect with us

News

KASITDA Ta Samar Da Sabbin Tsare-tsare Domin Inganta Ayyukan Ma’aikatar Lafiya A Kano 

Published

on

IMG 20260512 WA0008
Advertisements
ads

Daraktan Janar na hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta Jihar Kano (KASITDA), Dakta Bashir Abdu Muzakkari, ya kai ziyarar aiki ta musamman zuwa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano domin ƙarfafa shirin sauya harkokin gwamnati zuwa tsarin zamani na yanar gizo.

Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen aiwatar da Ajandar Sauyin fasahar zamani ta Kano 2025 zuwa 2030, wadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙaddamar domin inganta ayyukan gwamnati ta hanyar amfani da fasaha da ingantattun kayayyakin sadarwa.

Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman Gidan Yari Na Shekaru 75 

Yayin ganawar, Dakta Muzakkari ya jaddada muhimmancin amfani da fasahar zamani wajen inganta gudanar da harkokin lafiya, sarrafa bayanai, ƙarfafa ingancin cibiyoyi da kuma taimakawa wajen yanke shawara bisa hujjoji domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kano.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar da Ma’aikatar Lafiya wani muhimmin mataki ne na cika burin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina gwamnati mai amfani da fasahar zamani wadda za ta kasance mai inganci, gaskiya da kuma sauraron bukatun jama’a.

Dakta Muzakkari ya kuma bayyana cewa KASITDA ta samu jarin naira biliyan bakwai domin tallafa wa tsarin fasahar zamani a muhimman sassa uku na jihar, waɗanda suka haɗa da Ma’aikatar Lafiya ta Kano, Hukumar Tsare-tsare da Raya Birane ta Kano (KNUPDA) da kuma bangaren shari’a na jihar.

Advertisement

A cewarsa, jarin zai taimaka wajen samar da sabbin hanyoyin fasahar zamani, ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata da kuma kafa ingantaccen tsarin sarrafa bayanai domin bunƙasa ayyukan gwamnati da hidimomin jama’a.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko, Farfesa Salisu Muhammad; Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Asibitoci, Dakta Mansur Nagoda; da Sakatariyar Hukumar Kula da taimakekeniyar Lafiya, Dakta Rahila Mukhtar, tare da daraktoci da manyan jami’an KASITDA da na Ma’aikatar Lafiya.

Jami’an ma’aikatar sun yaba wa KASITDA kan ƙoƙarinta na bunƙasa kirkire-kirkire da sauyin fasahar zamani a harkokin gwamnati, tare da nuna shirinsu na yin aiki tare domin tabbatar da nasarar shirin sauya harkokin lafiya zuwa tsarin zamani.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending