News
Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano
Wata mata ta shiga hannun jami’an ’yan sanda a Jihar Kano bayan zargin banka wa mijinta da sabuwar amaryarsa tare da ’ya’yanta biyu wuta a unguwar Gidan Mai Alo da ke Hotoro a cikin birnin Kano.
Aminiya ta ruwaito cewalamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda ake zargin matar ta zuba fetur a kan mijin nata da amaryar tare da yaran kafin ta kunna musu wuta bayan ta kulle su a cikin daki.
An Rantsar Da Shugaba Yoweri Museveni Na Kasar Uganda A Karo Na 7
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa matar ta dade tana nuna bacin rai tun bayan da mijin nata ya kara aure kimanin makonni biyu da suka gabata, lamarin da ake zargin ya haddasa rikicin cikin gidan.
An ce wadanda abin ya shafa sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar, inda aka garzaya da amaryar da ’ya’yanta biyu zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cafke matar da ake zargi yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.
Lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin, inda da dama ke bayyana alhini tare da kira ga ma’aurata da su rika warware matsalolin aure cikin fahimta da lumana.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
