Connect with us

News

Faduwar Wayar Wutar lantarki Ya Yi Ajalin Yara 2

Published

on

Wutar Lantarki

Wasu yara biyu ’yan shekara bakwai, Oloyede Ayo da Clinton Koleola, sun mutu bayan sun taɓa wata wayar Wuta lantarki mai ɗauke da wuta da ta faɗo kan wani shago a yankin Idanre da ke Jihar Ondo.

Rahotanni sun ce yaran suna cikin shagon ne lokacin da wayar lantarkin ta faɗo kan ginin ba zato ba tsammani.

Rikicin Kabilanci Ya Yi Sanadiyyar Konewar Gidaje Kusan 340 A Taraba

Wani ganau ya ce bayan faɗowar wayar, yaran sun yi ƙoƙarin ficewa daga cikin shagon, amma suka yi kuskuren taɓa wayar lantarkin da ke ƙasa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu.

Faruwar lamarin na ranar Asabar ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

Daga bisani aka sanar da ’yan sanda game da lamarin, inda suka fara bincike kan musabbabin mutuwar yaran.

Advertisement

Kakakin ’yan sanda na Jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa, binciken farko ya nuna yaran sun mutu ne sakamakon lantarki yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga shagon da wayar lantarki ta faɗo a kansa.

Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta ƙaddamar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa lamarin.

Jami’in ya jajanta wa iyalan yaran, tare da tabbatar musu da cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending