News
Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano Ta Gayyaci Tijjani Gandu kan Zargin Karya Doka
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta gayyaci mawaki Tijjani Gandu domin amsa tambayoyi kan zargin karya dokokin hukumar yayin sakin wata waka.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ANIPR, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar 3 ga Oktoba, 2026, a madadin Shugaban Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha.
Maulidi Na Taimakawa Wajen Tunar Da Al’umma Halayen Annabi —Malam Ibrahim Khaleel
Sanarwar ta ce dokokin hukumar sun tanadi cewa duk wani mawaki ko marubuci ya gabatar da wakarsa ko rubutunsa ga hukumar domin tantancewa kafin a fitar da shi ga jama’a.
Hukumar ta ce manufar hakan ita ce tabbatar da cewa babu kalmomi ko abubuwan da za su iya haifar da tashin hankali ko tada zaune tsaye a cikin al’umma.
Ta ce dokar da ta kafa hukumar ta ba ta hurumin tantance wakoki da sauran ayyukan da suka shafi harkar fina-finai da dab’i a Jihar Kano.
“Hukumar ba za ta ci gaba da kallon wasu mutane suna karya dokokinta ba da sunan fadin albarkacin baki,” in ji sanarwar.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da bin doka da oda a cikin ayyukanta, tare da tabbatar da adalci ga dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da nuna wariya ko son kai ba.
Saboda haka, ta bukaci Tijjani Gandu da ya amsa gayyatar da aka yi masa, tana mai cewa kin amsa gayyatar na iya tilasta mata daukar matakan da suka dace bisa tanadin doka.
Haka kuma, hukumar ta yi kira ga mawaka, marubuta da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da bin dokokinta da ka’idojinta domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban harkar nishadi da adabi a Jihar Kano.
