Connect with us

News

Rundunar Sojin Ƙasa Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma’aikata Na Short Service

Published

on

WhatsApp Image 2026 08 11 at 15.55.40

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta buɗe shafin neman aikin soja na musamman, wato Short Service Combatant Commission (SSCC) Course 50/2027, ga ’yan Najeriya da suka cancanta.

Rundunar ta ce damar ta shafi fararen hula da kuma jami’an da ke aiki a halin yanzu, inda waɗanda za su yi nasara za a ba su mukami a sassan yaƙi da na tallafawa ayyukan yaƙi.

Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji

A cikin wata sanarwa da Rundunar Sojin Ƙasar ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa ɓangaren yaƙi ya haɗa da Dakarun Ƙasa da Dakarun Tankokin Yaƙi, yayin da ɓangaren tallafawa ya ƙunshi Dakarun Manyan Bindigogi, Injiniyoyi, Sadarwa da Sashen Binciken Sirri.

Rundunar ta buƙaci masu sha’awar neman aikin da su gabatar da takardunsu ta hanyar sahihin shafin yanar gizon ɗaukar ma’aikata na Rundunar Sojin Ƙasa.

Ta ce masu neman aikin su zaɓi SSCC a shafin, sannan su bi dukkan umarnin da aka bayar cikin taka-tsantsan.

Advertisement

Rundunar ta kuma yi gargaɗi ga masu neman aikin da su yi watsi da duk wasu shafuka ko sanarwar ɗaukar ma’aikata na bogi waɗanda ba su da izini.

Ta ƙara jaddada cewa masu neman aikin su dogara ne kawai da sahihan hanyoyin sadarwa na Rundunar Sojin Ƙasa domin samun ingantattun bayanai kan aikin ɗaukar ma’aikatan.

Haka kuma, Rundunar ta shawarci masu neman aikin da su riƙa bibiyar sanarwar ɗaukar ma’aikatan da za a riƙa gabatarwa ta gidajen talabijin da rediyo bayan fitar da sanarwar.

A cewar Rundunar, Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, ita ce ranar ƙarshe da za a karɓi aikace-aikacen neman aikin.

Domin ƙarin bayani, masu neman aikin za su iya kiran 07016874003 ko 07047340295, tsakanin ƙarfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, kowace rana.

Rundunar Sojin Ƙasa ta yi kira ga ’yan Najeriya da suka cancanta kuma suke da sha’awar yi wa ƙasar hidima da su yi amfani da wannan dama kafin cikar wa’adin neman aikin.

Advertisement

 

 

PRNIGERIA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending